Header Ads Widget

Header Ads

DAGA SAK, SAI BITA-DA-KULLI ?

Lallai kuwa za'a yita !!
Domin ga alama gidajen Yari (Prisons) na Jihar Katsina za'a cika su FAL da al'umma kamar yadda alamu suka nuna.
Babu irin jeka-ka dawo da bamuyi da Gwamnatin data shude ba. Duk da cewa ta ta6uka ayyukan alkhairi kuma masu muhimmanci in da can, amma sai da akayi mata luguden rubuce-rubuce har aka kaita kasa.
Sai gashi ayau wai mune wannan Gwamnatin zata yiwa #BitaDaQulli, sunci moriyar ganga ko?
Abinda suka kasa ganewa shine, Shekaru 4 kamar gyangyadin sa'o'i hudu ne. Kuma dama mulkin kama-kama ake. Idan yau ka kama, gobe dole ka saki ga wani shima ya kama; koda kuwa ba Jam'iyyar ku daya ba.
Kuskure ne babba wannan Gwamnati ke tafkawa wajen yin fada da masu rubutun social media musamman a wannan zamani da muke ciki. Domin kuwa ko shakka babu idan har hakan taci gaba da faruwa to kamar kuna da6awa kanku wuqa ne. Kuma lokaci na nan zuwa wanda zaku nemi taimako da agajin wadannan mutane, amma alokacin waje ya qure.
Idan har Gwamna Aminu Bello Masari yana da masaniya akan irin cin kashin kajin da ake yiwa marubutan social media a wannan Jiha kuma yayi shiru kamar bai san me ake ba, to lallai bai cika alqawarin da ya dauka na baiwa al'umma damar su fadi ra'ayinsu ba (freedom of speech). Idan kuwa bai sane, 'yan bani na iyane suke yi mashi shigar murtsutsu kuma ya kasa daukar mataki; to duka dai tagomashin yana akan shi.
SAK dai mun riga mun yi ta, kuma idan akwai dadi munji idan ma babu munji. Gaskiya Sak ita ce, ko Baba Muhammadu Buhari da kanshi bai jin dadin SAK a yanzu kuma bazai qara umartar mu da muyi taba. Kai wallahi idan ma yace muyi SAK zamu qeqashe muce masa A'A, sai mun duba cancanta.
Saboda haka ba wanda zai qara yi mana wata fankama da yaudara daga baya kuma azo ana tsattsagar mu don rashin ta ido. Idan zaku yi aikiwa al'umma kuyi idan kuma canje-canjen sunaye zakuyi to RANA DAI BATA QARYA......!! Mudai rubutu sai munyi, kuyi mana abin kirki mu fada, ku muzguna mana shima mu fada.
Kame kuma dama ba yau aka fara ba kuma ba yau za'a daina ba. Duk dai 'Dan daya hana uwarshi bacci............
Kwamared Yusuf Umar Dutsin-ma
Juma'a : 23-09-2016
elyusuf212@gmail.com
+2348031178528

Post a Comment

1 Comments