Kungiyar Hausa Hackathon Africa, mai rajin habbaka harshen hausa ta fannin abinda ya shafi Muradun Karni wato Sustainable Development Goals a turance, ta gudanar da babban gangami na matasa wanda ta yi ma taken ‘Katsina Youth Empowerment Summit’.
Taron, wanda ya samu halartar matasa daga waje da sakon birnin Katsina da makwabtan Jihohi; an yi shi ne a babban dakin taro na habbaka kasuwanci dake Makarantar Kimiyya ta Hassan Usman Katsina Polytechnic.
Taron ya maida hankali ga abubuwan da suka shafi kirkira da kuma salo na zamani wanda matasa zasu yi amfani da su wajen ganin sun daina zaman banza tare da samun rayuwar inganci mai dorewa.
Yusuf Umar Usman, wanda shine shugaban taron; ya yi bayanin muhimmancin harshen hausa wajen bunkasa harkar ilimi, kasuwan, noma, lafiya da kuma kimiyya da fasaha na wannan karni da muke ciki.
Malam Mustapha Shehu, wanda yayi Magana akan Digital Inclusion da yadda harkar technology take da muhimmanci idan aka bawa kowa dama a ciki. A inda Malam Abu Ali ya gabatar da kasida akan muhimmancin matasa su nemi jagorori nagari wadanda zasu tsaya masu tare da nuna masu hanyar daya dace su bi don samun dacewa bukatun rayuwa, musamman ma a harkokin sana’o’i da kasuwanci.
A bangare daya kuma, an gabatar da muhawara wadda aka yi ma taken ayyukan kwarewa wanda matasa ya dace su iya don dogaro da kai.
Shi dai wannan taro ya zamo irin shin a farko a Jihar ta Katsina, kuma yanzu haka shirye shiryen gudanar da irin shi a Jihohin Kano da Kaduna da kuma Biranen Zindar, Agadez na Jamhuriyar Nijar sun fara kankama.
Dr. Moussa Garba, wanda shine ya assasa wannan kungiya; yayi Magana daga birnin Paris na Faransa inda yayi godiya ga mahalarta taron tare da jawabi akan yunkurin kungiyar Hausa Hackathon Africa wajen hada muradun karni, harshen hausa da kuma kirkire-kirkire na kimiyya.
1 Comments
Very interesting development
ReplyDelete